
Gwamnatin tarayya ta sanar da kulle shafukan yanar gizo guda Miliyan 13 saboda dora abubuwan da basu dace ba.
An kulle shafukan ne dake kan TikTok, Facebook, Instagram, and X, bayan da wadannan kafafe suka bada hadin kai wa Gwamnatin Najeriya wajan kai rahoton irin wannan shafukan.
Wadannan shafukan sun sabawa dokar Najeriya wadda hukumomin Nigerian Communications Commission (NCC), the National Information Technology Development Agency (NITDA), da the National Broadcasting Commission (NBC) suka samar ta amfani da kafafen sada zumunta.
Rahoton yace an goge shafukan ne dan tabbatar da ana tsaftace irin abubuwan da ake yadawa a kafafen sada zumunta.
Wakiliyar Gwamnatin tarayya, Hajiya Umar ta jinjinawa kamfanonin sadarwar saboda bada hadin kai wajan goge irin wadannan shafukan.