
Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ‘yan sanda, Sanata Abdulhamid Ahmed Malam Madori, ne ya bayyana haka yayin taron gwamnati da jama-a a Kafin Hausa.
Ya ce an sanya kudin a cikin kasafin kudin 2025, kuma majalisar dattawa ta riga ta amince da dokar kafa makarantar wadda ake jiran sa hannun shugaban kasa.
Sanata Malam Madori ya bayyana cewa shi ne ya dauki nauyin gabatar da kudurin kafa makarantar wadda za ta taimaka wajen samar da kwararrun ‘yan sanda na zamani domin inganta harkar tsaro a fadin kasar nan.
Ya nuna cewa ya riga ya bai wa ofishin ‘yan sanda na Kafin Hausa sabuwar motar Hilux tare da gyara da samar da kayayyaki ga ofishin da gidajen ‘yan sanda, domin karfafa gwiwar jami’an da ke aiki a yankin. Bugu da kari, ya tallafa wa matasa da mata sama da 8,000 a Kafin Hausa, yayinda ya bayar da fiye da Naira miliyan 5 don kammala babban masallacin Juma’a a gari.