
Kasar Amurka ta bayyana cewa, Albashin Naira 77,000 da Gwamnatin Najeriya ke biya yayi kadan, ba zai fitar da ‘yan kasar daga Talauci ba.
Amurkar ta bayyana hakane a wani rahoto data fitar.
Tace duk da gwamnatin tarayya ta nunka Albashin da ake biya a baya amma hakan yayi kadan matuka ya fitar da ‘yan kasar daga Talauci.
Rahoton yace, abin damuwar ma shine Gwamnatin Najeriya bata iya biyan mafi karancin Albashin a lokuta da yawa sannan kuma Gwamnatocin jihohi suma basa iya biya saboda karancin kudi.
Sannan Rahoton yace wannan mafi karancin Albashin yawanci ma’aikata ba zasu sameshi ba saboda yawanci kamfanoni basu da ma’aikata da yawa inda wasu kuma manoma ne da sauran kananan ma’aikata.
Hakan na zuwane a yayin da ake shirin karawa shugaban kasa, da sauran manyan ‘yan siyasa Albashi.