
Mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da tsarin daukar ma’aikata karkashin shirin Masu Tsaron Daji (Forest Guards) a matsayin wani bangare na yaki da matsalolin tsaro a karkashin shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Tinubu.
Ribadu ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Laraba yayin kaddamar da sababbin motocin aiki 46 da aka raba wa sassan tsaro daban-daban a fadin kasar nan. Ya ce tsarin zai baiwa kowace jiha damar daukar ma’aikata tsakanin 2,000 zuwa 5,000 gwargwadon karfin su.
Ya ce shirin zai taimaka wajen kare al’ummomi, dazuzzuka da albarkatun kasa na Najeriya. Ribadu ya kara da cewa akwai sauye-sauye masu ma’ana da ake samu kullum a fannin tsaro, wadanda koda ba su fito fili ba, ana ganin tasirinsu a rayuwar al’umma.