Alum daya daga cikin abubuwan da ake amfani dasu ne wajan tsaftace ruwa da sauran magungunan gargajiya.
Mata na amfani da Alum a shekaru Aruru da suka gabata musamman wajan matse gabansu.
Bari mu duba amfaninsa dalla-dalla.
Amfanin alum a gaban mace
Da yawan mata sukan yi amfani da Alum wajan matse gabansu shekaru aru-aru da suka gabata.
Kuma har a yanzu ma wasu na amfani dashi, saidai a yayin da yake yima wasu aiki, wasu kuwa baya musu aikin yanda ya kamata.
Alum ya kasu kashi-kashi, bari mu duba kowanne da yanda ake amfani dashi.
Alum na Gari a Gaban Mace
Alum na gari farine dake saurin narkewa a cikin ruwa.
Yanda ake amfani da alum na gari a gaban mace
- Ana zuba daya bisa hudu na cokalin shan shayi a cikin kofi, sannan a sa ruwa
- A juya sosai har sai Alum din ya bace.
- A yi amfani da wannan ruwa a wanke gaban mace a hankali.
- Bayan an gama a wanke da ruwa me kyau.
Alum na Dutse a gaban mace
Akwai kuma Alum na dutse wanda shima farine ko kuma ace garai-garai wanda ake ganin tsakiyarsa.
Yanda ake amfani da alum na dutse a gaban mace
- Ana wankeshi da ruwa me tsafta
- Sannan a gogashi a jikin gaban mace, kada a tura ciki.
- A wanke da ruwa me tsafta bayan an gama.
Amfanin alum a gaban mace
- Yana sa gaban mace ya matse.
- Yana magance cutukan bacteria da kuma hana cutuka shiga gaban mace.
- Yana taimakawa wajan rage kaikai a gaban mace.
- Yana hana gaban mace wari.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:
A shafin twitter zaku same mu a @hutudole
A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole