Friday, December 5
Shadow

Duk me tunanin Tinubu ba zai sake cin zabeba a 2027 mahaukaci ne lamba 1>>Inji Farfesa Haruna Yarima

Farfesa Haruna Yarima wanda tsohon dan majalisar tarayya ne ya bayyana cewa, duk me tunanin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba zai sake cin zabe a shekarar 2027 ba mahaukaci ne.

Yayi fadi hakane a martaninsa ga masu cewa, Tinubu idan bai sauke Kashim Shettima a matsayin mataimaki ba ya dauko wani musamman Kirista ba zai ci zaben 2027 ba.

Farfesa Yerima ya bayyana cewa, wannan magana ba gaskiya bane domin kuwa kamin shugaba Tinubu ya dauko Kashim Shettima a matsayin mataimaki, saida ya lura da abubuwa da yawa.

Yace dan haka a yanzu ko da wani zai kawo maganar a canja Kashim Shettima a matsayin mataimaki, Shugaba Tinubu ne da kansa zai fara cewa bai yadda ba.

Karanta Wannan  Ina goyon bayan ciren tallafin man fetur da shugaba Tinubu yayi>>Inji Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *