
Kungiyar kwadago ta NLC tace shirin gwamnati na cire tallafin wutar Lantarki zai jefa dubban ‘yan Najeriya cikin wahalar rayuwa, sannan zai durkusar da kasuwanci da yawa da yanzu haka suke fama.
Sakataren riko na kungiyar, Comrade Benson Upah ne ya bayyana hakan inda yace cire tallafin, zai karawa rayuwa tsada a Najeriya.
A baya dai Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya tabbatar da cewa, Gwamnati zata cire tallafin wutar saboda ‘yan Najeriya su rika biyan ainahin kudin wutar da suke sha.
Saidai bayan cire tallafin man fetur hakannya jefa mutane da yawa cikin wahalar rayuwa.