
Babbar Kotun tarayya dake Lagos ta kwace hannun jari da darajarsa ta kai Naira Miliyan 246 daga hannun tsohon soja wanda ya rike hukumar kula da kadarorin hukumar sojojin Najeriya, NAPL watau Major-General U.M. Mohammed (Retd.).
Mai shari’a, Justice Chukwujekwu Aneke ne ya bayyana hakan inda yace a wallafa maganar a gidajen jaridu inda yace kwace kadarorin na wucin gadi ne dan haka suna kiran duk wanda yake da hujjar da zata hana a kwace kadarorin dindindin yayi magana.
A sabuwar shari’ar da aka yi wadda mai shari’a, Justice Dehinde Dipeolu yayi hukunci, yace a yanzu an kwace hannun jarin dindindin daga hannun tsohon sojan.