
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, yasan Gyare-Gyaren tayar da komadar tattalin arziki da yake yi sun jefa ‘yan Najeriya a rayuwar wahala.
Yace amma maganar gaskiya gyaran ya zama dole kuma nan gaba za’a ga amfaninsa.
Shugaban ya bayyana hakane a yayin ganawar da yayi da ‘yan Najeriya mazauna kasar Brazil inda ya nemi hadin kansu wajan ciyar da Najeriya gaba.
Ya kuma nemi a hada kai dan zaman lafiya da kawo ci gaba ga Najeriya.