Monday, December 16
Shadow

Wata nawa ake haihuwa

Sanin sanda zaki haihu abune me dadi. Ga bayanin masana ilimin kimiyyar lafiya kan lokacin haihuwa.

Yayin da mutane mafi yawanci an fi sabawa da kirgen watanni idan aka zo maganar haihuwa, masana ilimin kimiyyar lafiya na amfani da kwanaki da makonnine.

A cewar masana kiwon lafiya, cikakken daukar ciki har zuwa a haifeshi, makonni 40 ne, wanda yayi daidai da watanni 10.

Nasan da yawa zasu sha mamaki da jin wannan bayani, to bari kuji abinda masana kimiyyar lafiya suka ce.

Yawancin mata suna sanin suna da ciki ne bayan basu ga jinin al’adarsu ba, wanda a wannan lokacin kuma mace ta riga ta kai sati 4 da daukar cikin.

Karanta Wannan  Yadda ake gane fitsarin mai ciki

To a wannan lokacin kuma saura sati 36 mace ta haihu, wanda shine yayi daidai da watanni 9, yanzu kun gane dalilin koh?

Sanin ranar da zaki haihu, yawanci likitane ke wannan lissafin, kuma ba lallaine ya zamo daidai ba, kina iya haihuwa kamin ko bayan ranar da suka gaya miki.

Saidai idan kin rike ranar farko ta jinin al’adarki da ya wuce, zaki iya lissafa ranar da zaki haihu a wannan shafin, danna nan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *