
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mayar da martani ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kan sukar da ya masa a gidan talabijin na Channels TV.
Shugaban ya mayar da martanin ne ta bakin me magana da yawunsa, Bayo Onanuga ta kafar X.
Ya rubuta cewa a shekarun baya, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yace shekaru 4 sun yiwa shugaban kasa kada ya gyara Najeriya ko ya kawo ci gaba amma yanzu yana sukarsa.
Yace amma duk da haka ya kawo abubuwan ci gaba Najeriya sosai.
Misali an samu habakar arziki sosai ta bangaren kasuwar hannun jari inda aka samu karuwar dukiya data kai naira Tiriliyan 26.