
Rahotanni sun bayyana cewa, rashin biyan kudin haya yasa an kulle ofisoshin jakadancin Najeriyar a kasashen Waje da dama.
Sanarwa daga ma’aikatar kasashen waje ce ta tabbatar da hakan daga bakin me magana da yawun ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa.
Sanarwar tace gwamnati na sane da lamarin inda ta alakantashi da karancin kudi.
Ofisoshin jakadancin Najeriya a kasashe da yawa sun kasa biyan ma’aikata da gudanar da ayyukansu saboda yanda lamarin rashin kudin yayi kamari.
Saidai ma’aikatar tace tuni Gwamnatin tarayya ta dauki aniyar magance wannan matsala domin an ma fara aikawa ofisoshin jakadancin da kudade dan warware wannan matsala.