
Wani matashi me suna Omar ya bayyana cewa, Habu Dan Damisa, Watau dan dabar da yayi kaurin suna a Kaduna wanda ake zargin jami’an tsaro da kashewa ya tuba.
Yace su sun san Malam Habu, yace tun kamin hawan mulkin El-Rufai ya daina kisa da kwace.
Yace shekaru 3 da suka gabata babu wanda zai ce maka ya ga Habu yayi kisa ko kuma ya yi kwace.
Yace shikenan kuma sai ace mutum ba zai yi laifi ya tubaba?