
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, bai gaji ko sisi daga hannun mahaifinsa ba.
Ya bayyana hakane a wata tsohuwar hira da gidan jaridar Bloomberg suka yi dashi a shekarar 2020.
Dangote yace bayan rasuwar mahaifinsa an bashi gadonsa amma sai ya kyautar da kudin, yace kuma yana alfahari da hakan.
Sannan ya kara da cewa ya yiwa kawunsa aiki kadan inda daga baya ya bar Kano zuwa Legas inda ya fara sayar da sumunti
Yace a wancan lokacin ana shigo da siminti ne cikin Najeriya.