Friday, December 5
Shadow

Ban yi kuskure ba wajen zaɓen Kashim a matsayin mataimaki – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yaba da jajircewar mataimakinsa, Kashim Shettima, wanda ya bayyana da mutum mai amana da gaskiya da yake jin daɗin aiki da shi.

A wata sanarwa da ya fitar kan taya mataimakin nasa murnar cika 59 a duniya, Tinubu ya ce, “tun da na sanka har zuwa yanzu, ba ka nuna gajiyawa wajen aiki tuƙuru domin sake gina ƙasarmu. A dukkan muƙaman da ka riƙe a baya, ka nuna jajircewa wajen aiwatar da abubuwan da suka dace duk runtsi duk wahala.”

Tinubu ya ce yana godiya bisa irin goyon bayan da yake samu daga Shettima, “lokacin da na zaɓe ka a matsayin mataimakina, na san ban yi zaɓen tumun-dare ba, na san na ɗauko nagartacce wanda Najeriya za ta yi alfahari da shi. Kullum a aikinka na mataimaki, kana ƙoƙari wajen kawo shawarwari da tsara sababbin abubuwa da za su taimaka mana wajen sauke nauyin da muka ɗauka.”

Karanta Wannan  Hankula sun tashi bayan da aka dauke wutar lantarki a kasar Faransa na tsawon awanni 5

“Ban yi ba kuskure ba wajen zaɓenka a matsayin mataimaki. Tare da kai mun fara aikin dawo da martabar Najeriya ta hanyar gyare-gyare da matakan da muka fara ɗabbaƙawa a shirinmu na Renewed Hope Agenda,” in ji shi, inda ya ƙara da cewa alaƙarsu ta wuce maganar aiki kawai.

Tinubu ya ce suna samun nasarori da yawa tare, “ka sake nuna mana irin nasarorin da za a samu idan aka sadaukar kai tare da haɗin kai wajen ciyar da ƙasa gaba, wanda shi ne abin da ya kama masu zama shugabanni za su koya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *