
Bayan rasuwar kasurgumin dan daba dake kaduna, Habu Dan Damusa, an rika samun mutane wasu na Allah wadai wasu kuma na jinjinawa gareshi.
Wata me suna Rabeeat data bayyana cewa ta sanshi tace matsalar ba ta rashin Ilimi bace
Tace yaransa guda 4 duk mahaddata Qur’anine inda tace PA dinsa ma mahaddacin Qur’anine.
Tace Addu’a ce kawai mafita inda tace me unguwarsu da ya rika tsine musu shima yaransa duk sun shiga daba.
Tace dan haka ida mutum ya musu Addu’a, kamar yawa ‘ya’yansa ne.
