
Rahotanni sun tabbatar da cewa farashin CNG wanda Gwamnatin Najeriyar ta kawo bayan cire tallafin man fetur tace shine zai maye man fetur ta kuma bayar da tallafi akansa farashinsa yayi sauki sosai a yanzu ta cire masa tallafi kuma har farashinsa ya nunka.
Rahoton da muke samu daga Punchng ya tabbatar mana da cewa, farashin na CNG ya tashi ya kai Naira 450, ga manyan motoci inda kananan motoci kuma ke sha akan farashin 380.
Shugaban shirin na CNG, Michael Oluwagbemi yaki daukar waya dan yin bayanin dalilin cire tallafin.
Saidai wani na kusa dashi da bai so a kira sunansa ya tabbatarwa da Punchng chire tallafin inda yace yanzu tashoshin CNG din na sayar da shi a farashi mabanbanta amma ya danganta da kalar motar da mutum ya je sayen CNG din da ita.