Wannan dai ana ganin zai rage radadin da jama’ar yankin ke fuskanta, yayin da kasar da ke yammacin Afirka ke fama da hauhawar farashin kayayyaki.
Matakin shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu, na cire tallafin man fetur lokacin da yake karbar rantsuwar kama aiki, ta haifar da tsadar rayuwa da kuma tsadar man a sassan kasar.