
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kama hanyar zuwa kasashen Faransa da Ingila inda zai yi hutu acan.
Gwamnan Imo dana Legas da sakataren Gwamnatin tarayya na daga cikin wadanda suka mai rakiya zuwa filin jirgin.
Fadar shugaban kasa tace shugaban zai kwashe kwanaki 10 ne yana wannan hutun.