Friday, December 5
Shadow

A sanya Najeriya cikin addu’o’in Maulidi – Remi Tinubu

Mai ɗakin shugaban Najeriya, Remi Tinubu ta buƙaci al’ummar Musulmi su sanya ƙasar cikin addu’o’in neman zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Cikin wata sanarwa da ta fitar albarkacin ranar Maulidin, Remi Tinubu ta aike da saƙon barka ga al’ummar musulmai a faɗin ƙasar.

A rana irin ta yau a duk shekara ne miliyoyin Musulmi a faɗin duniya ke bikin domin murnar zagayowar ranar da aka haifi Annabi Muhammadu (S.A.W).

”Wannan na tuna mana yin koyi da kyayawan halayen Annabi a rayuwarmu ta yau da kullum, ta hanyar nuna soyayya da tausayawa da mutuntawa da haɗin kai”, in ji shi.

Ta ƙara da cewa yana da kyau ”mu ci gaba da yi wa ƙasarmu addu’o’in zaman lafiya da ci gaba”.

Karanta Wannan  Zargin wulakanta Naira: Kotu ta saka ranar da za ta yankewa Murja hukunci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *