Akwai alamu da yada dake nuna ciki ya jai haihuwa:
Zaki iya jin zafi sosai kamar na lokacin al’ada.
Zaki ji mahaifar ta matse sannan zata saki.
Hakan zai iya ci gaba da faruwa, yana zuwa yana tafiya duk bayan mintuna 5, kuma lokaci na tafiya hakan na kara tsananta.
Da kinji haka to a kira ungozoma ko kuma a kaiki asibiti, Haihuwa ta zo.
Zaki iya jin ciwon baya sosai.
A yayin da kike da ciki, wani ruwa me yauki yana taruwa ya kulle kofar mahaifarki, to a yayin da kika zo haihuwa, wannan ruwan zai fito waje, idan kika ganshi, me yauki ne kuma Pink to haihuwa ta zo, saidai wasu na haihuwa ba tare da ganin ruwan ba.
Amma masana kiwon lafiya sun ce rashin ganin ruwan ka iya zama alamar cewa akwai matsala tare da ke ko abinda zaki haifa. Dan haka ya kamata a nemi ungozoma ko likita.
Idan kika ga jini ya biyo baya sosai to a kira ungozoma ko a je asibiti, watakila akwai matsala.
Bayan fitowar wannan ruwa, zaki iya haihuwa nan take, ko kuma kina iya yin doguwar nakuda, ko ki fara nakuda bayan awanni ashirin da hudu da fitar ruwan ko kuma zata dauki kwanaki.
Zaki iya jin kamar kina son yin kashi, hakan na faruwa ne saboda jaririn na kokarin turo kanshi waje.
Jini zai iya zuba.
Abinda ke cikinki zai rage motsi.
Da kinji wadannan alamu to a gaggauta kiran Ungozoma ko likita.
Yaya zaki yi idan haihuwa ta zo?
Zaki iya tashi ki dan yi tattaki idan kina son yin hakan.
Zaki iya shan ruwa ko lemu dan ki ji karfin jikinki.
Zaki iya cin cincin, cake, ko wani abu makamancin hakan.
Ki rika nishi a hankali da kuma nutsuwar jikinki.
Kisa a rika shafa miki bayanki, hakan na kawo saukin zafin nakudan.
Masana kiwon lafiya sun ce zaki iya shan Paracetamol. Yana taimakawa kuma bashi da illa lokacin nakuda.
Zaki iya yin wanka da ruwan dumi.
[…] wannan lokaci ne ya kamata ki samu ilimi kan haihuwa saboda kina kusa da […]