
Tauraruwar BBNaija, Farida Sultana Auduson Ibrahim wadda aka fi sani da Sultana ta bayyana cewa ita musulmace.
Ta bayyana hakane a hirarta da Zita.
‘Yar shekara 25 data fito daga jihar Adamawa amma tana zaune a Abuja me tallar kayan sawa tace ta taso gidansu Mahaifinta musulmi mahaifiyarta Kirista.
Tace mahaifinta dan jihar Adamawa ne musulmi kuma mahaifiyarta ‘yar jihar Cross River ce kirista, tace ta rika zuwa coci da masallaci a lokacin tana karamar yarinya sannan har an mata wankan tsarki na Kiristanci wanda tace kuma an bata sunan Josephine.
Sultana tace amma daga karshe ta zabi Musulunci saboda ta ga shine yafi dacewa da ita.