Friday, December 5
Shadow

NNPP ta kori Abdulmumin Kofa daga jam’iyyar

Jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano ta kori ɗanmajalisar tarayya Abdulmumin Jibrin Kofa daga jam’iyyar tana mai zargin sa da cin amanarta.

Shugaban jam’iyyar na Kano, Hashim Dungurawa ya faɗa wa BBC cewa sun kori ɗanmajalisar mai wailtar mazaɓar Kiru da Bebeji saboda dalilai na cin amana da kuma tallan wani ɗantakara.

“Mun same shi da cin amanar jam’iyya a matakai daban-daban,” in ji Dungurawa. “Na farko, mun same shi da tallata ɗantakarar shugaban ƙasa na wata jam’iya da ba namu ba.

“Na biyu, ya ce zai iya fita daga jam’iyyar. Wannan ba ƙaramin cin amana ba ne. Na uku, ba ya biyan kuɗin haraji na jam’iyya, duk da cewa akwai doka cewa duk wata akwai abin da zai bayar domin cigaban jam’iyyar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Abin na ban Haushi yanda maza ke ta rububi akaina>>Inji Wannan Budurwar

“Na huɗu, ba ya zuwa mazaɓarsa. ‘Yan mazaɓarsa kan yi kusan wata biyar ba su ji ɗuriyarsa ba.”

Zuwa yanzu ɗanmajalisar bai mayar da martami ba.

Ɗanmajalisar ya kai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na APC ziyara a watan Yuli, kuma a kwanan nan aka jiyo shi yana bayyana goyon baya ga shugaban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *