
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa, har Dakin Allah, Ka’aba an je an tsine masa dan haka babu abinda zai sameshi.
Ya bayyana hakane a sabon Bidiyon da ya saki inda yake mayar da martani game da hotunanda da aka dauka a wajan wani biki daya halarta.
An ga Gfresh da kuraje cike da fuskarsa, ba kamar yanda aka saba ganinsa fuska fresh ba kamar ta jarirai a Bidiyonsa.
Gfresh yace an mamayesu shi da Murja Kunya an yi amfani da wayoyi masu arha aka daukesu hotuna, yace dan haka shi ya fara tunanin kara tsaro a kusa dashi.
Yace kuma babu abinda zai sameshi dan mai abinda yafi haka bai kunyata ba.
Gfresh yace an mayar dashi wani Salmanu, amma yace duk da haka kaf ‘yan fim da mawaka babu wanda zai iya tara jama’ar da zai tara.