Wednesday, January 15
Shadow

Cikin wata biyar

Duk da yake cewa kowace mace da irin yanda ta ke daukar cikinta amma a wata 5 da daukar ciki, za’a ga girman cikinki ya bayyana.

Jikinki zai fara canjawa yana daidaituwa da yanda cikinki ke kara girma.

Ga wasu alamu da ke nuna cewa cikinki ya kai wata 5:

Kafafunki zasu Kumbura: saboda nauyin da kika kara saboda cikin dake jikinki, kafafunki zasu iya kumbura, kwanciya a daga kafa sama yana taimakawa wajan magance wannan matsala.

Ciwon kwankwaso: Saboda yanda cikinki ke fitowa, bayanki zai rika shigewa ciki wanda hakan zai iya kawo miko ciwon kwankwaso.

Juwa: A yayin da jaririnki ya ke girma, yawan jinin dake gudana musamman zuwa kanki zai iya raguwa wanda zai sa ki ji juwa.

Karanta Wannan  Gwajin ciki na sati daya

Mura: Zaki iya fuskantar Mura, hancinki ya toshe ko kuma yayi ta yoyo, kai yana ma iya fitar da jini.

Zaki rika manta abubuwa, misali zaki manta inda kika ajiye wayarki, ko wata ajiya da kikayi, duk wannan alamu ne na ciki a wata biyar.

Zaki iya shan wahala wajan bacci: Saboda girman da cikinki ke karawa, zaki iya shan wahala wajan yin bacci. Mun yi rubutu kan Yadda mai ciki zata kwanta

Zaki iya jin cikinki yana dan ciwo yana dan matsewa kadan.

A wata 5, abinda ke cikinki ya fara ginuwa sosai saboda motsin da zako ji yana yi, ya fara bacci yana tashi, kai har ma motsin da ake a waje zai iya ji kuma yayi martani akai.

Karanta Wannan  Alamomin cikin wata takwas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *