
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Sanata Uba Sani ya musanta ikirarin cewa, Tsohon Gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai uban gidanda ne a siyasance kuma shine ya koya masa soyasa.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda aka tambayeshi me zai ce game da ikirarin El-Rufai na cewa shine ya koya masa siyasa?
Gwamna Uba Sani yace baya son mayar da martani akan wani mutum daya dan hankalinsa na kan jihar Kaduna.
Yace amma Shugabab kasa, Bola Ahmad Tinubu da tsohon lauya, marigayi Chief Gani Fawehinmi sune iyayensa a siyasa sune suka koya masa siyasa.