
Hukumar wutar Lantarki ta Najeriya reshen jihar Legas, ta fitar da sanarwar cewa, wutar Lantarki ta samu matsala kuma ba’a san me ya haifar da hakan ba.
Hukumar tace tana aiki tukuru dan dawo da wutar inda ta baiwa abokan huldarta hakuri.
A baya dai, Hutudole ya kawo muku rahoton yanda wutar Lantarkin Najeriya gaba daya ta samu matsala wanda hakan ya jefa kasar cikin duhu.