
Matashiya, Iftihal ta dauki hankula sosai musamman a kafafen sada zumunta saboda an saba ganinta da hijabi, Kwatsam sai gata tare da mawaka tana rawar badala.
Da farko dai mutane sun yi tsammanin ba ita bace, amma daga baya sai na kusa da ita suka tabbatar da cewa itace.
Idan mutum ya duba shafinta na Tiktok, kullun a cikin Hijabi take Bidiyo ba zaka taba tsammanin zata aikata hakan ba.
Saidai wata majiya tace tabbas Iftihal ce a wannan Bidiyon wakar da suka yi da su Soja Boya wanda dama ya saba yin wakokin batsa.
Da yawan masu sharhi a kafafen sada zumunta sun bayyana rashin jin dadin abinda Iftihal ta aikata inda wasu suka rika janyo hankalinta ta gujewa irin waccan rayuwar: