
Tauraron me wakar Batsa wanda ya fito daga jihar Sokoto, wanda aka fi sani da Soja Boy ya bayyana cewa hada addini da harkar Nishadi ko rawa da waka Izgili ne.
Ya bayyana cewa Addini da rawa da fim da waka ba zasu taba haduwa ba har abada.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi.
Soja Boy dai yana shan suka sosai a wajan mutane musamman ma kwanannan shine yayi waka da matashiyar ‘yar Fim iftihal Madaki wadda aka saba ganinta da Hijabi amma rana daya aka ganta tana rawa da mawaka.