
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya cire tallafin man fetur ne dan ci gaban Najeriya.
Yace shugabab ya yi hakane ba tare da damuwa ko za’a sake zabensa a shekarar 2027 ba.
Ya bayyana hakane a wajan wani taron tsaffin ‘yan majalisar tarayya daga kudancin Najeriya wanda ya faru a jihar Ogun.
Yace tabbas cire tallafin ya kawo wahalhalu amma na dan lokacine.
Ya luma kawo misalai irin na tallafin karatun dalibai da sauransu wadanda suka taimaka wajan inganta ilimi da saukaka radadin da mutane ke ji.