
Matatar man fetur ta Dangote zata rage farashin man fetur dinta zuwa daga Naira 865 zuwa Naira 841 akan kowace lita a jihar Legas da sauran Jihohin Yarbawa.
Hakanan matatar zata rage farashin kowace lita zuwa Naira 851 a Abuja da kuma jihohin Kwara, da Edo.
Hakan na zuwane a yayin da Matatar man ta Dangote ke shirin fara kaiwa gidajen sayar da man fetur man kyauta da motocin tanka na dakon Man fetur din data siyo daga kasashen waje.
Rikici tsakanin matatar man fetur ta Dangote da sauran ‘yan kasuwar man fetur ya ta’azzara sosai inda suka ce sai ya shiga kungiyarsu amma shi kuma yace hakan ba zata yiyu ba.