
Me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa, yana goyon bayan cire tallafin man fetur da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi.
Ya bayyana hakane a wajan wani taron marubuta da aka gayyaceshi.
Sarkin Yace Da ba’a cire tallafin Man fetur din ba da Najeriya ta durkushe.
Sarki Sanusi na daga cikin na gaba-gaba wajan bayar da shawarar daina biyan tallafin man fetur shekaru da dama da suka gabata.