
Tsohon kakakin majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ya lalata Darajar Naira.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro da ya halarta inda yace Buga kudin Naira sama da Naira Tiriliyan 22.7 ne ya jawowa Kudin Naira karyewa.
Yace an rika amfani da damar karbar dala wasu suna arzuta kansu fiye da kima a lokacin mulkin Buharin.