
Hukumar Shirya jarabawar kammala sakandare, NECO ta fitar da sakamakon jarabawar kuma kaso 60 cikin 100 na wadanda suka rubuta jarabawar sun yi nasara.
An saki sakamakon jarabawar ne kwanaki 54 bayan rubutata.
Ragistara na NECO, Farfesa Ibrahim Wushishi ya sanar da sakamakon jarabawar inda yace dalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarabawar.
Wanda suka ci jarabawar kuma sun kai 818,492 wanda hakan yake nufin kaso 60.26 cikin 100 sun ci jarabawar. Wadannan wadanda suka ci lissafi da turanci ne.
Hakanan yace wadanda kuma suka ci 5 credit sun kai 1,144,496, wanda hakan ke nufin kaso 84.26.