
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa tin kamin ya hau mulki akwai yunwa a Najeriya.
Shugaban ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa, Daniel Bwala a yayin da ake hira dashi a gidan talabijin na TVC.
Bwala yana martanine ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da ya soki Gwamnatin kan halin da mutane ke ciki.
Bwala yace tun a lokacin da aka baiwa Najeriya ‘yancin kai akwai yunwa a Najeriya, yace ba a lokacin Tinubu aka yi wakar Najeriya Jaga-jaga ba dan haka tun kamin hawansa akwai matsaloli da suka mamaye kasarnan.
Yace amma ‘yan adawar ba zasu fadi irin nasarorin da gwamnatinsu ta samu ba sai inda aka samu matsala.