
Gwamnatin tarayya tace ta rabawa gidaje Miliyan 8.5 Tallafin kudi Naira Biliyan 330 a fadin Najeriya.
Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana hakan.
Ya bayyana hakane ranar Laraba a Abuja inda yace gwamnati ta dawo da raba tallafin bayan Gyare-Gyaren da aka wa tsarin.
Yace suna raba kudadenne saboda ragewa mutane radadin tsadar rayuwa inda yace mutane Miliyan 15 suke son rabawa.
Yace zuwa yanzu sun raba kudin a gide Miliyan 8.5 inda suke biyan Naira dubu shirin da biyar duk wata.
Ministan yace sauran ma zuwa karshen shekarar nan za’abasu.