
Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyara jihar Kaduna a gobe, Juma’a idan Allah ya kaimu.
Shugaban zai halarci daurin auren dan Sanata Abdulaziz Yari me suna Nasirudeen Yari da amaryarsa, Safiyya Shehu Idris.
Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar a ranar 18 ga watan Satumba.
Hakanan sanarwar tace shugaban kasar zai kuma kaiwa matar tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari ziyara.
Sannan a Ranar Juma’ar dai ne shugaban zai koma Abuja.