
Tauraruwar BBNaija, Sultana wadda ‘yar Asalin Jihar Adamawa ce ta sake jawo cece-kuce.
Sultana ta jawo cece-kuce ne bayan Bidiyon ta da aka ga tana rawa tsirara a gaban abokanta da suke yin BBNaija din tare.

Wasu dai musamman daga kudu sai jinjina mata suke suna cewa ta iya rawa amma wasu na mamakin ashe dama ‘yan matan Arewa sun iya sheke aya haka?
Sultana dai ta taba bayar da labarin cewa mahaifinta Musulmine amma mahaifiyarta kirista ce daga kudancin Najeriya.
Karanta Wannan Na yi kokari a yanzu duk talaucin talaka yana cin shinkafa a gidanshi>>Shugaba Tinubu
Tace ta taso tana Sallah kuma tana zuwa coci amma dai daga baya ta zabi ta zama musulma.