
Ana zargin Wani mutum a Kano da yin Alfasha da matar amininsa.
Rahotanni sun ce aminin babu abinda baiwa abokin kasa ba da ya ci amanarsa, Asali ko lokacin aurensa kusan shine yayi komai.
Amma da yake yana tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, kuma a Legas yake zaune da iyalinsa, da zarar ya yi tafiya, sai abokij ya shirya musamman ya je Legas ya rika lalata da matar abokin nasa.
Hon. Danbaban Gawuna ne ya bayar da wannan labari inda yace abokinsu ne lamarin ya faru dashi.
Yace sun bashi shawarar ya saki matar, yace ko da bayan ya saketa ta koma gidansu, abokin bai daina bibiyarta ba.
Gawuna yace tsohon mijin yasa a daukar masa hoton abokin nasa idan yaje wajan tsohuwar matar tasa dan ya kafa hujja, yace shine wata rana da ya je, wani yaro a unguwar ya daukeshi hoto ya turawa tsohon Mijin.
Wani Karfin hali, shine abokin ya kai yaron ofishin ‘yansanda dake Bomfai.
Gawuna yace shine suka je ake case.
Yace nan gaba idan abu yayi kamari zasu kafe hoton wannan Kwarto dan kowa yayi hankali dashi.