
Yawan kudin da ‘yan Najeriya suka tarawa matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu na zagayowar ranar Haihuwarta sun kai Naira N20,456,188,924.93.
Matar shugaban kasar ta nemi ‘yan Najeriya su tura tallafi yayin da take bikin cikarta shekaru 65 da haihuwa.
Tace za’a yi amfani da kudinne wajan kammala ginin hedikwatar dakin karatu na kasa.