Daga watan Janairu na shekarar 2024 zuwa 14 ga watan Yuni Mutane 65 ne suka kamu da cutar amai da gudana inda guda 30 suka mutu.
An samu cutarne a kananan hukumomi 96 da ke jihohi 30 a fadin Najeriya kamar yanda hukumar kula da cututtuka ta kasa, NCDC ta bayyanar.
Hukumar ta bayyana hakane a sanarwar data fitar ranar Alhamis dan ankarar da mutane kan lamarin inda tace a yi hankali saboda zuwan ruwan sama.