Friday, December 5
Shadow

Matatar man Dangote ta kori duka ma’ikatanta na Najeriya bayan da suka shiga kungiyar kwadago ta PENGASSAN

Rahotanni sun ce matatar man fetur ta Dangote ta kori duka m’aikatanta ‘yan Najeriya.

Matatar tace ta yi hakanne dan canja fasalin ayyukanta.

Saidai hakan na zuwane bayan da ma’aikatan suka shiga kungiyar kwadago ta ma’aikatan man fetur ta PENGASSAN.

Jimullar wadanda aka kora daga aikin sun kai mutane 1000 saidai matatar bata kori ma’akatan dake mata aiki ‘yan kasashen waje ba.

Rikici da rashin fahimtar juna yai kamari tsakanin Dangote da kungiyar ta PENGASSAN inda ta zargi Dangoten da hana ma’aikatan matatarsa shiga kungiyar wanda tace hakan ya sabawa dokokin aiki a Najeriya.

Saidai Dangote ya sha cewa shiga kungiyar kwadagon zabine ba abune na dole ba.

Karanta Wannan  Jihar Gombe ta kulla yarjejeniya da kamfanin kasar China dan samarwa da kanta wutar Lantarki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *