
Matatar man fetur ta Dangote tace daga yau, zata daina sayar da man fetur dinta da Naira.
Ta sanar da cewa man data tanada dan sayarwa a Naira ya kare.
Matatar tace hakan ba zai ci gaba ba.
Matatar tace wadanda suka bayar da kudinsu dan sayen man da Naira a yanzu suna iya neman a mayar musu da kudadensu.
Sannan tace idan an samu chanji aka ci gaba da sayar da man da Naira zasu sanar da abokan hulda.