
Shugaban ya Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Sakamakon wahalar da ‘yan Najeriya ke sha ya fara bayyana.
Shugaban ya kuma jinjinawa ‘yan Najeriyar bisa nuna dauriya da irin matsin da suka samu kansu a ciki.
Shugaban ya bayyana hakane ranar Juma’a a wajan nadin sarautar Olubadan of Ibadanland a garin Ibadan.
Tinubu yace wahalar da ‘yan Najeriya ke sha saboda tiyatar da yakewa Najeriya ne kuma ba zata zama ta banza ba, nan gaba za’a moreta.