
Malamin Addinin Islama, Sheikh Sani Rijiyar Lemu ya bayyana goyon baya ga Malam Lawal Triumph game da zargin da ake masa na yiwa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Batanci.
Sheikh Sani yace Kalaman da malam yayi suna tare dashi suma akan irin wannan fatawar suke.
Yace da ake cewa wai idan ba’a kama Lawal Triumph ba, shima Abduljabbar a sakeshi, yace idan so suke a saki Abduljabbar su fito kawai su fada ba sai sun yiwa wani sharri ba.