
Rahotanni sun ce zaman sulhu da aka yi tsakanin wakilan kungiyar PENGASSAN da na Matatar Dangote an tashi ba tare da cimma matsaya ba.
Gwamnatin tarayya ce ta kira zaman wanda aka fara ranar Litinin da misalin karfe 4 p.m..
Ministan kwadago, Mohammed Dingyadi da karamar ministan Kwadago, Nkiruka Onyejeocha sun halarci zaman wanda aka shafe awanni 9 ana yi.
Minista Dingyadi yace za’a dawo ci gaba da zaman da misalin karfe 2 p.m. na ranar Talata.
Gwamnatin tarayya tace tana duba abinda wannan rikici zai jawowa Najeriya ne shiyasa take kokarin sulhunta Bangarorin Dangote da PENGASSAN.