
Rahotanni sun ce daga yau, 1 ga watan Oktoba, Hukumar kula da shige da fici ta Najeriya zasu fara kame da hukunta wadanda suka shigo Najeriya bizarsu ta kare basu fita ba da wadanda kuma suna shigo ba tare da takardu ba.
Wadanda aka kama da laifi, zasu iya fuskantar hukuncin mayar dasu kasashensu ko kuma cinsu tara.
Wanda aka kama ya dade a Najeriya tsawon watanni 3 bayan shigowa kuma takardunsa sun kare, zai biya tarar Dala $15 kullun.
Ko kuma a bashi zabin hanashi shigowa Najeriya na tsawon shekaru 2.
Sai kuma wadanda suka tsaya a Najeriya na tsawon watanni 3 zuwa shekara 1, su kuma za’a musu hukuncin biyan tarar dala $15 kullun ko kuma hanasu shigowa Najeriya na tsawon shekaru 5.