
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi Allah wadai da kwamishinan ‘yansandan jihar, Inda yace ya basu kunya saboda kin halartar bikin ranar ‘yancin Najeriya.
Gwamna Abba yace Kwamishinan ya dauki matakai da suka nuna cewa yana goyon bayan wata jam’iyya.
Gwamnan yace shine Gwamna sannan shugaban tsaro na jihar Kano kuma Allah ne ya bashi, dan haka babu wanda ya isa ya kwace mai.
Gwamnan yayi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya cire Kwamishinan ‘yansandan daga jihar Kano na kawo musu wani.
Kalli Jawabin Gwamnan a kasa: