
Malamin Addinin Musulunci, Dr. Sharafdeen Gbadebo wanda yayi wa’azi da yarbanci ya bayyana cewa, yin Gwajin kwayoyin halitta na DNA haramun ne a Musulunci.
Ana yin gwajin DNA ne dan gano da na wanene musamman idan aka samu gaddama tsakanin mata da miji, mijij yana zarginta da kawo mai dan da ba nashi ba.
Malamin yace a addini babu tsarin yin gwajin DNA.
Yace abinda addini ya zo dashi, rantsuwa ake yi tsakanin matar da mijin.