
Matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta bayyana cewa, an samu ci gaba sosai a mulkin Mijinta, Bola Ahmad Tinubu.
Ta bayyana cewa, a yanzu an daina kiran Najeriya da kasar cin hanci da rashawa. Tace idan ta fita zuwa kasashen waje, aka ce daga Najeriya take mutane na son magana da ita.
Ta bayyana hakane a yayin ziyarar da ta kai jihar Gombe inda ta kaddamar da wasu ayyukan ci gaba.
Ta yi kira ga ‘yan Najeriya dasu mayar da hankali wajan yada labarai masu kyau game da kasar.